Article
Livestreaming · 4 min read
Live Streaming ya zama ɗaya daga cikin manyan hanyoyin isar da saƙo kai tsaye a Social Media. A yau ana amfani da shi wajen taruka, wa’azi, conferences, interviews, podcasts, shirye shirye na kafafen yaɗa labarai da sauran muhimman abubuwa.
Amma har yanzu mutane da yawa suna kallon Live Streaming a matsayin kawai ka ɗauki waya, ka kunna Facebook ko wata manhaja, sannan ka fara Live.
Wannan ma Live Streaming ne, kuma yana da wuraren da ya dace a yi amfani da shi. Amma idan ana son samar da aikin da zai fito da tsari da ƙwarewa irin ta kafafen yaɗa labarai na zamani, akwai hanyoyin da za a ɗaga darajar aikin fiye da haka.
Ba sai kana da TV Station ba
Ɗaya daga cikin abubuwan da fasahar zamani ta sauƙaƙa shi ne yadda mutum ko ƙaramar media team za su iya samar da Live Production mai kyau ba tare da sai suna da cikakken TV studio ba.
A matakin farawa, idan kana da waya mai camera mai kyau da computer mai ƙarfin gudanar da aikin, za ka iya fara gina tsarin Live Streaming mai kyau.
Daga baya, gwargwadon buƙata da ƙarfin aikin, za ka iya ƙara cameras, microphones, capture devices, lighting, audio equipment da sauran kayan aikin production.
Abu mafi muhimmanci shi ne fahimtar tsarin aikin da kuma yadda ake haɗa waɗannan abubuwan wuri guda.
vMix da OBS Studio suna buɗe ƙarin dama
Daga cikin software da za su iya taimaka maka wajen ɗaga darajar Live Streaming akwai vMix da OBS Studio.
Maimakon Live ɗinka ya tsaya kan camera guda kawai, waɗannan manhajoji suna ba ka damar tsara yadda broadcast ɗinka zai fito.
Za ka iya amfani da cameras fiye da ɗaya, ka riƙa sauyawa tsakaninsu yayin Live.
Za ka iya saka sunan mai magana a ƙasan screen.
Za ka iya saka logo.
Za ka iya saka ticker.
Za ka iya nuna hotuna, videos, presentations da sauran graphics yayin da ake Live.
Za ka iya tsara scenes daban daban gwargwadon abin da ake gabatarwa.
Haka kuma, idan tsarin aikinka ya buƙata, za ka iya haɗa remote participants da sauran sources cikin production ɗinka.
Wannan shi ne abin da yake fara mayar da Live Streaming daga kawai kunna camera zuwa Live Production mai cikakken tsari.
Kyakkyawan Live ba software kaɗai ba ne
Amma akwai kuskuren da bai kamata mu yi ba.
Samun vMix ko OBS Studio kaɗai ba yana nufin kai tsaye za ka samar da broadcast mai inganci ba.
Software kayan aiki ne.
Har yanzu kana buƙatar fahimtar camera framing, audio, lighting, graphics, internet connection, computer performance da yadda ake gudanar da production yayin da ake Live.
Musamman audio. Mutane za su iya jure hoto da bai kai matuƙar kyau ba na ɗan lokaci, amma idan ba sa jin abin da ake faɗa yadda ya kamata, Live ɗin zai yi wahalar bi.
Haka kuma, internet connection mai ƙarfi da stable yana da matuƙar muhimmanci. Kyakkyawan graphics da cameras ba za su ceci broadcast ba idan connection ɗin da ake amfani da shi ba zai iya ɗaukar stream ɗin yadda ya kamata ba.
Ka fara da abin da kake da shi
Ba manufar wannan rubutun ba ce a ce sai ka tara manyan kayan aiki kafin ka fara.
Akasin haka.
Idan kana da waya mai kyau da computer mai kyau, kana da abin da za ka iya fara koyon tsarin da shi.
Ka fara da camera guda.
Ka koyi OBS Studio ko vMix.
Ka fahimci yadda ake shigar da video da audio.
Ka koyi yadda ake saka logo da lower third.
Ka fahimci scenes da switching.
Ka yi practice ba tare da kana Live ba.
Da zarar ka fara fahimtar waɗannan abubuwan, sai ka riƙa ƙara wa setup ɗinka ƙarfi gwargwadon buƙatarka.
Inganci yana ƙara darajar saƙonka
Idan ana gabatar da taro, programme ko wani muhimmin saƙo, yadda aka gabatar da shi yana da tasiri ga yadda mutane za su karɓe shi.
Kyakkyawan hoto, tsaftataccen audio, graphics masu kyau da switching mai tsari suna taimakawa wajen sa mai kallo ya ji cewa ana gabatar masa da aikin da aka shirya da muhimmanci.
Wannan shi ne dalilin da ya sa nake ganin lokaci ya yi da za mu ƙara ɗaga matsayin Live Streaming a Social Media.
Ba wai kawai mu kasance muna yin Live ba.
Mu kasance muna samar da Live Production mai kyau, mai tsari, kuma wanda ya dace da matsayin abin da muke gabatarwa.
vMix da OBS Studio suna daga cikin kayan aikin da za su iya taimaka mana mu cimma wannan, amma abu mafi muhimmanci shi ne mu koyi yadda ake amfani da su da kyau, mu yi practice, sannan mu ci gaba da inganta aikinmu a hankali.
Continue exploring
More practical ideas and professional conversations.